NASIHA TA!
Sunday, October 27, 2013 1:04:08 PM
Ka yo wa kanka nasiha
Ka nisanci 'yan masifa
Ka zamanto mai son da'a
Kaurace wa su matsafa
Ka kadaita Shi ko Allah
Ba a karyata tasa siffa
Nasa jalla sunayensa
Ya siffanta da su fa!
Kar ka hawo ta Jahmu
Hanyar mafalsafa fa!
Ta kauce wa hikima
Hanyar tawili ce fa!
Hanya ce karkatatta
Ta su ma'abota fafa
Hanyar mu'utazilawa
Hanyar asha'irawa fa!
Wasu siffar sun kore
Wasu tsantsa tawili fa!
Wasu wai da sunan tsira
Su noke, Mufauwidha fa!
Kasance tare da sunnah
Tserace wa bidi'a fa!
Ka ga tafarkin salafu
Shi ne tsira garen fa!
26102013ibs.
