My Opera is closing 3rd of March

Ibrahim Lawal Soro

English,Arabic and Hausa.

HAKA ABIN YAKE GUDANA [KASARMU DA KASASHEN DUNIYA]

[1] Da kungiyar al-Qaedah [Khawarij] ta je musu, kafin isowarta wadanda suka jahilci manhajin magabata na kwarai sukai ta yayata ta, har matasa suke neman hanya duk matsinta zuwa gareta, wasu sun isa wasu da Boko-Haram [Khawaarij] ta iso Najeriya -Allah ya kara karya ta, ya shafe ta daga ban kasa- dama an rage musu hanya sai suka fada cikinta, saboda mashayar su daya.

[2] Da tashoshin talabijin suka yawaita, maɓarnata cikin rigar malunta suka riƙi ragama, wadanda suka yi nisa da sanin manhajin magabata na kwarai, makusanta ga sharri da ƙira zuwa ga ɓarna, wadanda suka kwace jagorancin matasa a hanunsu, ta hanyar tasoshin talabijin nasu, sai ɓarna ta yaɗu a doron ƙasa, gata muna gani a Syria, Libya, Tunusia da Egypt.

Irin abin da ya je musu shi ne ya fara zuwa mana: bayyanar wasu malamai masu gurbataccen manhaji, masu cutar neman suna, su na shayar da matasa gubarsu, su na farautar hankulansu, sun bace sun batar, su na goyon bayan ta'addanci a Egypt, su na barrantar da kansu ga barinsa a Najeriya, alhali sun san mashayar su daya ce.

Lallai wannan matsala ba karama ba ce, don ma Allah ya rufa asiri; ba kowa daga cikin wadanda zasu iya fadawa tarkon su keda halin kallon su ba.

Cikin su akwai wadanda suke ganin halaccin zanga-zanga; wai hanyar bayyana ra'ayi da kokawa ce, haka shedaninsa ya fada masa.

Cikin su akwai wadanda ke ganin shugaban Najeriya ya halatta a fito a yake shi, fita daga karkashinsa ba Khawarijanci ba ne, haka manhajin khawarijanci da ya sha a hanun malamansa ya motsa da irin wannan batacciyar magana, wacce sababinta ake rasa rayuka, ɓarna take maye gurbin gyara, tashin hankali ke korar zaman lafiya da lumana.

Cikinsu akwai wanda yake kiran malaman Sunnah na hakika, wandanda suke tsaye kan duga-dugen su, wadanda suke hakuri da cutarwar ƴan bidi'ah da ire-irensa, yake kiransu yan raba kai, yake tsoratar da dalibansa saurararsu, yake ingiza su saurarar mabarnata: masu rushe ijma'i, masu karya wa Salaf, ƴan reni da karyar fahimtar yau, tare da cewa fatan malaman da yake cewa kar a saurare su, kokarin su: iri-irensa masu gurbataccen manhaji su gyaru, irin na khawarijawa su watsar, irin na mu'utazilawa su jefar, amma duk da irin wannan gata, shi ya dauka hakan raba kai ne.

Cikin su akwai wadanda shi ma jagora a fannin gyaran akida ce, amma bayan ambatonsa ya watsu, kimarsa ta bazu, cikin zukatan mabiya ta samu zama, wajen ma'abota hukunci sun shaida, saboda haka sai ya juya baya, ma'abota kira da gaske yake kushewa, masu kokarin shayar da al'umma alheri yake kokarin rushewa, saboda ya cika burinsa, dama addini shi ne makamin duk wani dan neman duniya, Allah ka shirya halin sa.

[Abu Abdirrahman]

دعوة السلفية

Write a comment

You must be logged in to write a comment. If you're not a registered member, please sign up.

February 2014
M T W T F S S
January 2014March 2014
1 2
3 4 5 6 7 8 9
10 11 12 13 14 15 16
17 18 19 20 21 22 23
24 25 26 27 28