My Opera is closing 3rd of March

lamadobi

ALLAH (SWT) YACE: "HARAMUN NE
KA SHIGAR WA IYAYEN KA, KO
MUHARRAMANKA BA TARE DA YI
MUSU SALLAMA BA" HATTA
IYALANKA BA ZA KA SHIGA GARE SU
BA SAI DA SALLAMA.
(Q: NUR 59.)
"Ya ku wadanda sukayi imani!
Wadannan da hannuwanku na
dama suka mallaka da wadanda
basu isa mafarki ba daga cikin ku,
su nemi izini sau uku, daga
gabannin Sallar alfijir, da lokacin da
kuke ajiye tufafin ku, saboda zafin
rana, kuma daga bayan Sallar Isha'i.
Su ne al'aurori uku a gare ku, babu
laifi a kanku kuma babu a kansu a
bayan su. Su masu kewaya ne a
kanku, sashen ku akan
sashe." (Surutun Nur, aya ta 58)
A takaice ladubban shiga gida sune,
dukkan yaron da ya balaga dane ko
bawa, kada ya shiga gida ko dakin
mahaifin sa ko uban gidan sa a a
bayan sallama, har sai in an amsa
da ya shigo, in ance ya koma, ya
koma. In kuma yana zaton ko ba'a
ji bane, to ya maimaita sau uku.
Neman izini wajibi ne ga yayanka
baligai a lokutan nan uku, kamar
yadda yazo a aya ta 59, daga
gabanin sallar Alfijir, lokacin tsakar
rana, wato lokacin da ake ajiye
tufafi saboda zafin rana da kuma
bayan sallar isha'i.
Wannan aya ta wajabta mana,
musamman mata da su koyawa
yayansu da kanne ko yan uwa dake
zaune a gida tare da su da masu
aiki, da su dauki tarbiyya irin
wadda Al'qur'ani mai girma yazo
da ita, da kuma sunnar manzon
Allah tsira aminci su tabbata a gare
shi. Halayyar mu ce a yanzu da aje
wa mutum ziyara a ko wane lokaci,
ko kuma a banka kai cikin daki
babu sallama , in ba a amsa ba, sai
mutum ya tafi yana fushi, yana
kunkuni wai anyi masa wulakanci.
Ya 'yan uwa Musulmi, mu ji tsoron
fushin Ubangiji bana mutum ba,
fushin Mutum ko zagin sa, bazai
cutar da kai da komi ba. Yayin da
ka bi dokar Ubangiji, to zakayi
rayuwar ka cikin kwanciya hankali
babu kunci. Sannan ina Nasiha ga
yan uwa maza da su daina zuwa
gidajen abokai a lokutan Da Allah
ya hana.
"Babu laifi a gare ku da kuci abincin
juna, ko 'dai 'dai, ko a kwano daya,
a gidajen kawunan ku, 'yan
uwanku har da abokan ku, amma
in anci a tashi, kada a tsaya hira,
kuma kada aje kafin lokacin da aka
gayyace ka, ka zauna har sai an
gama abincin, wannan baya
halatta, yayin da muka bi dokar
Allah, to baza mu sami kuntata a
kanmu ba, insha Allah. Yana daga
dabi'un mu a yanzu a ki watsewa
bayan gayyata, ko bayan aboki yaci
abinci, sai ya tsaya hira, har masu
gida su kosa.
Bahaushe yace, wai bayan ci zama
tsegumi, tafiya rashin kunya, to
umurnin Allah zaka bi ko son rai?
Shima bahaushen ai cewa yayi
zama tsegumi, wanda yake
haramun ne, cewa kuma tafiya
rashin kunya, shima kuskure ne,
domin yaci karo da umurnin Allah.
Allah ya samu a bisa hanya
madaidaiciya, ya nuna mana
gaskiya gaskiya ce ya bamu ikon
binta, ya nuna mana karya karya ce
ya bamu ikon guje mata.

Lawal Madobi

Write a comment

New comments have been disabled for this post.